✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kammala aikin Gadar Neja kafin Kirsimeti —Gwamnati

Gwamnati ta rade-radin da ke cewa sai shekarar 2024 za a kammala aikin

Gwamnatin Tarayya ta ce aikin Gadar Neja ta biyu da take yi a yanzu, zai kammala nan da lokacin bikin Kirsimeti.

Mataimakin Kwanturolan Ma‘aikatar Ayyuka ta Jihar Anambra, Mista Seyi Martind ne ya bayyana hakan a wata ganawa da Aminiya a Awka, babban birnin jihar ranar Litinin.

Martins ya ce ana gab da kammala zagayen farko na aikin da kusan kaso 95, wanda ya kai nisan kilomita 1.6.

Haka kuma, ya ce sabanin labarin da ake yadawa cewa sai shekarar 2024 za a kammala, a karshen shekarar 2022 ne gwamnati ke sa ran gama shi.

Ya tabbatar wa al’ummar da ke wucewa ta Gadar Nejan cewa, ba za su fuskanci cunkoson ababen hawa ba a yayin bikin Kirsimetin bana.

“Ba a kai ga fara kashi na biyu na aikin ba, amma gwamnati ta yanke shawarar bude titin da zarar an kammala kashi na farko”, in ji shi.

Acewarsa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tabbatar da matafiya ba su wahala ba saboda aikin a lokutan bikin.