✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a kara mafi karancin albashin ma’aikata a 2024

Ministan Kwadago da Ayyuka Chris Ngige ya ce shirye-shirye sun yi nisa don kara mafi karancin albashi a shekarar 2024. Ngige ya kuma gargadi kungiyoyin…

Ministan Kwadago da Ayyuka Chris Ngige ya ce shirye-shirye sun yi nisa don kara mafi karancin albashi a shekarar 2024.

Ngige ya kuma gargadi kungiyoyin kwadago da su daina tsoma kansu a harkokin gwamnati da kuma nada mukamai.

Ya kuma ce ‘ya‘yan kungiyar na karya dokar da ta tilasta wa duk wani sabon dan kungiya samun horo na musamman a makarantar horon kwadago ta (MINILS).

Kazalika a taron Kungiyar Kwadago na Kasa karo na 13 da aka gudanar ranar Talata a Abuja, ya ja hankalin ‘yan kwadagon da su tabbatar da gwamntocin jihohi na aiwatar da Dokar Diyyar Ma’aikata ta 2010 (ECA) da doka ta ce a biya su.