✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kara wa Abuja megawatt 800 na lantarki

Za a kara wa tasoshin wutar lantarki na Dawaki da Apo da Kuje da Lugbe da kuma Wumba

Shirye-shirye sun yi nisa na kara inganta hanyoyin samar da wutar lantarki a Abuja da kewaye.

Ministan Makamashi, Abubakar Aliyu, ya ce aikin zai kara karfin wutar lanatarkin da kamfanin TCN ke samarwa a yankin da megawats 1,000.

Ministan ya ce, Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ne ya ke aikin wanda aka yi masa lakabi da ‘Aikin Zoben Abuja’.

Ya kuma ce, kungiyar taimaka wa kasashe ta gwamnatin Faransa (AFD) ce ta dauki nauyin aikin da aljihunta.

Ana sa rai aikin zai samar da karin karfin lantarki wanda za a kara wa tasoshin wutar lantarki na Dawaki da Apo da Kuje da Lugbe da kuma Wumba, wanda za a kaddamar a watan disamba.

Ya sanar da hakan yayin da yake jawabi ga ’yan jarida bayan ziyarar gani da ido da ya kai wurin aikin samar da wutar lantarki ga birnin a ranar Juma’a.