✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a karrama dan jaridar Daily Trust da FFK ya ci zarafinsa

An shirya gagarumin taro domin karrama Eyo Charles a matsayin Jajirtaccen Dan Jarida

Wata kungiyar farar hula mai suna Shayau Sarkin Fada a Jihar Zamfara za ta karrama wakilin jaridar Daily Trust a jihar Kuros Riba, Eyo Charles, da kyautar ‘Jajirtaccen Dan Jarida’.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Alhaji Sha’aya’u Sarkin Fada, a Gusau ranar Asabar.

Kungiyar ta ce yadda dan jaridar ya iya kame kansa yayin dambarwar shi ne ya ja hankalinta cewa ya cancanta ta karrama shi.

Ya ce, “Halin dattaku da sanin yakamata da Mista Charles ya nuna ya kara karfafa mana gwiwa kan cewa jar yanzu akwai jajirtattun ’yan jarida a kasar nan.

“A matsayinmu na cikakkun ’yan Najeriya, mun yi amanna in har da gaske FFK mai fafutukar kishin kasa ne kamar yadda ya ke ikirari, to kamata ya yi ya amsa tambayar da aka yi masa ba wai ya bige da zage-zage ba.

“Saboda haka mu a matakinmu mun yanke shawarar shirya gagarumin taro don karrama wannan dan jaridar da zarar mun ji daga gare shi”, inji kungiyar.

A makon da ya gabata ne dai Eyo ya fuskanci cin zarafi da zagi daga tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Femi Fani-Kayode, bayan ya yi masa tambaya a kan wanda yake daukar nauyin tafiye-tafiyen da yake yi zuwa jihohi domin duba ayyuka yayin wani taron manema labarai a birnin Kalaba.