✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe karin biliyan N600 a gyaran matatun mai

Bayan biliyan N276 da gyaran matatun ya ci a shekara uku Najeriya za ta kashe biliyan N600

Bayan kashe Naira biliyan 276 kan gyaran matatunta na man fetur daga 2015 zuwa 2018, Gwamnatin Tarayya na shirin kashe karin Naira biliyan 600 domin gyaran su daga farkon 2021.

Gwamnatinn ta kashe Naira biliyan 152 kan gyaran matatun daga shekarar 2013 zuwa 2017, idan za a iya tunawa.

Aminiya ta gano cewa lalacewar matatun man na daga cikin dalilan raguwar kudaden shigar gwamnati da karin farashin man fetur a cikin gida.

Bayan cire hannun gwamanti a harkar mai a baya-bayan nan da ya haifar da karin farashinsa, Minista a Ma’aikatar Albarkatun Mai, Timipre Sylva ya ce karin ba shi da makawa saboda farashin mai a kasuwar duniya ne ke yanke yadda za a sayar da shi a cikin gida.

Sai dai masana harkar sun ce da matatun na aiki to da tattalin arzikin kasar ba samu matsala sosai ba, hatta a lokacin annobar coronavirus.

Wasunsu na ganin gyaran matatun na iya fitar da Najeriya daga kangin shigo da mai daga ketare, wasu kuma na ganin matatun “sun tsufa sosai da za a yi ta gyarawa”.

Don haka suka shawarci gwamnati, duba da yadda kimiyya da fasaha ke sauyawa, da ta gina sabbin matatu na zamani masu matsakaitan girma.

Damuwa kan gyaran matatun

Yayin da ake ta kai ruwa rana kan karin farashin mai, Gwamnatin Tarayya na kokarin kwantar da kurar da cewa za ta farfado da matatun su rika aiki da akalla kashi 90 na karfinsu cikin shekara uku.

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kolo Kyari ya ce matatun kasar guda hudu (Kaduna, Warri, Fatakwal da Indorama, Eleme) na da jimillar karfin tace ganga 444,000 na mai a kullum.

A jawabinsa, ya ce da gangan aka rufe su saboda rashin yi musu cikakken gyara da manyan garambawul.

Duk da cewa an kashe sama da biliyan N276 wurin gyaran su daga shekarar 2015, Kyarri ya ce rashin yin gyaran da ya dace ya rage karfin matatun, wanda hakan ne ya kawo bukatar a yi musu muhimman gyare-gayre da garambawul.

“Ana bukatar kowace matata ta yi aiki na akalla kashi 90 na karfinta.

“Dakatar da gyare-gyaren ya sa babu yadda za a yi su iya aiki na kashi 90 din karfinsu.

“Mun kiyasta za su yi aiki na kashi 60 amma kuma hakan ba zai biya bukata ba.

“Muna so su yi aiki yadda ya kamata ne shi ya sa za mu yi musu cikakken gyara”, inji shi.

Ya ce a watan Mayun 2020 aka samu injiniyoyi na cikin gida daga Kamfanin Ayyukan Injiniya na Kasa (NETCO/KBR) karkashin NNPC da za su yi aikin matatun mai na Warri da Fatakwal.

Za a kashe Dala biliyan 1.5 (Naira biliyan 576.75) wurin gyaran matatar Fatakwal wanda aka kulla yarjejeniyar biya ta hanyar bayar danyen mai a maimakon kudi.

Aikin, mai suna Project Eagle ya samu goyon baya daga Bankin Shige da Fice na Afirka (Afreximbank).

Matatun mai na Kaduna da Warri

Bayan haka, za a kashe kudaden da ba a kai ga bayyanawa ba wajen gyaran matatar mai ta Kaduna da ta Warri.

A watan Agustan 2020, Kamfanin Matatar Mai na Kaduna (KRPC) ya yi shirin kashe tashar wutar lantarkinsa domin yin gyara a matatar.

Manajan Darektan KRPC, Injiniya Ezekiel Osarolube ya ce manyan shugabannin NNPC sun kosa su ga an fara an kuma kammala gyaran matatar.

Majiyar ta ce an yi nisa wurin kokarin ganin an ba wa kamfanonin da hukumar kula da sayayyar gwamnati (BPP) ta tantance sun fara aiki a matatar ta Kaduna da takwararta ta Warri.

Bututan mai na bukatar gyara

Aminiya ta gano cewa baya ga matatun, su ma bututan da ke kawo musu danyen mai da kuma zuwa ma’ajiyan tataccen man suna bukatar gyara.

Rahoton NNPC na watan Yuli da ta fitar ranar Alhamis ya nuna an fasa bututan mai a wurare 36, sabanin sau 33 da aka fasa a watan Yuni.

Hakan na nufin fasa bututan mai ya karu da kashi 9% a cikin wata guda.

Bututan mai da suka hada matatun da ma’ajiyarsa na: Atlas Cove-Mosimi da kuma Aba-Enugu na da kashi 28%; PHC-Aba na da kashi 14% sai kuma sauran masu kashi 31%.

Rahoton ya ce NNPC da al’ummomi masu makwabtaka da bututan da sauran masu ruwa da tsaki na ta kokari wajen yakar matsalar fasa bututun mai.

NNPC ta ce a 2023 za ta kammala aikin gyaran matatun man da za ta fara a farkon 2021.