✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe N1.2bn don gina manyan makarantu 18 a Arewa maso Gabas

Za a gina su ne a jihohi shida na yankin

Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya (NEDC) ta ce za ta gina wasu manyan makarantun zamani a jihohi shida na yankin.

Shugaban hukumar, Manjo Janar Paul Tarfa (mai ritaya), ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, yayin da yake gabatar da jawabi a Fadar Shugaban Kasa karo na 50, wanda tawagar yada labaran Shugaban Kasa ta shirya a Abuja.

Acewarsa, rashin ilimi ne ya haifar da matsalar tsaron da yankin ke fuskanta.

Ya kuma ce, “Muna magana ne kan manyan makarantun zamani da muke fatan za su dakile matsalolin tsaro, domin kowa ya san kungiyar Boko Haram na yaki ne da ilimin boko.

“Wannan ya sa muka zauna muka tattauna kan hanyoyin da za mu cigaba da bada ilimin na.

“Sai muka bijiro da wadanan makarantun na firamare da sakandare. kuma za mu gin adaya a dukkanin mazabu shida na yankin