✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe N175m wajen kawata sha tale-tale da gadar sama a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da Naira miliyan 175 da za ta batar wajen kawata ginin gadar sama da sha tale-talen Dangi da ke kan…

Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da Naira miliyan 175 da za ta batar wajen kawata ginin gadar sama da sha tale-talen Dangi da ke kan titin Gidan Zoo daura da Titin Zariya daf da Masallacin Aliyu Bin AbuTalib.

Kwamishinan Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya ce kudin da za a batar na daga cikin kwangilar sama da naira biliyan 4 da Majalisar Zartarwa ta Gwamnatin ta bayar tun daga farkon aikin har zuwa karewarsa.

Sauran kudaden da aka fitar sun hadar da naira miliyan 42.8 domin samar da gadaje da katifu a dakunan kwanan dalibai a Jami’ar Kimiya da Fasaha ta Jihar da ke Wudil.

Ya ce an kuma fitar da Naira miliyan 17.8 domin ginin magudan ruwa da sauran aikace-aikace na dakile matsalolin zaizayar kasa da ambaliyar ruwa a garin Lakwaya da Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar.

Ya kara da cewa Majalisar ta kuma tanadi Naira miliyan 198 domin sake gina Titin Gashash da Titin Otel din Daula tare da ware wasu Naira miliyan 529 domin samar da injina da kayan aiki na zamani a wasu manyan asibitoci biyar da ke fadin Jihar.