✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a kashe N4.5bn don gyara titunan Abuja da buga takardun jarabawa

Majalisar ta amince a ware N2.9bn don buga takardun jarabawar.

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), ta amince da kashe naira biliyan 4.5 wajen buga takardun jarabawa da gyaran tituna a wasu yankuna na birnin tarayya Abuja. 

Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan yayin da gana wa da manema labarai a fadar Shugaban Kasa bayan kammala zaman Majalisar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.

Mallam Adamu wanda ya kasance tare da takwaransa na Ma’aikatar Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya ce Majalisar ta amince a ware naira biliyan 2.9 domin buga takardun jarabawa da samar da muhimman kayayyakin aiki.

Ministan ilimi ya ce, za a bawa kamfanoni takwas kwantaragin buga takardun jarabawar da a za a yi amfani da su a jarabawar kammala matakin karatun sakandire karami da babba.

“Kamar yadda kowa ya ke da masaniya ce wa, an dage rubuta jarabawar a wannan lokaci sakamakon halin da muka samu kanmu na ’yar hatsaniya a wadannan kwanaki,” inji Ministan.

A nasa bangaren Ministan birnin tarayya, Muhammed Bello, ya bayyana wa manema labarai ce wa, Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince da kashe naira biliyan 1.6 N1,619,701,391.14, wurin gyara da sabunta wasu tituna da inganta su a wasu garuruwa da ke wajen birnin tarayya.

Bello, ya ce Majalisar ta amince a kashe naira N900,294,304.75 don gyaran wasu hanyoyi a yankin Gwagwalada, inda aka bawa kamfanin Messrs Teleview International Nig. Limited kwangilar aikin da ake sa ran kammala shi cikin watanni shida masu zuwa.

Kazalika, Ministan ya bayyana cewa an ware naira N719,407,086.38 wurin gyaran wasu titunan Kwali da ke Abuja, inda aka bawa kamfanin Messrs Sahabi Liman Sons Nig. kwangilar yin ayyukan cikin watanni shida.