✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe N863bn don yakar talauci — Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Buhari ce ta bullo dasu da nufin rage wa ’yan kasar radadin talauci.

Gwamnatin Najeriya za ta kashe naira biliyan 863 wurin gudanar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma na karshen shekara.

Shirye-shirye ne na musamman da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo dasu da nufin rage wa ’yan kasar radadin talauci.

Shirin National Social Investments Programmes (NSIP) da ya kunshi shirin N-Power da Conditional Cash Transfer Programme (CCT), da kuma shirin raba basussuka ga kananan ’yan kasuwa zai lakume naira biliyan 410.

Za a kuma kashe karin naira biliyan 300 kan wasu shirye-shiryen na daban ga al’umma a karkashin kulawar Ma’aikatar Ayyukan Jin Kai da Kare Afkuwar Bala’i.

Tun a shekarar 2016 ne gwamnati mai ci a Najeriya ta bullo da shirye-shiryen tallafa wa ’yan kasarta don rage musu radadin matsin rayuwa da suke ciki.

Kuma a 2020 abubuwa sun dada nauyi ga ’yan Najeriya bayan bullar annobar Coronavirus, da ta yi illa ga tattalin arziki.