✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kawo karshen ta’addanci a 2022 —Zulum

Zulum ya dakatar da albashin ma'aikatan lafiya da suka yi fashin aiki.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ce a shekarar 2022 za a ga bayan ayyukan ta’addanci da suka hana jama’ar jihar da makwabtanta sakat na tsawon shekara 12.

Zulum ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ziyarci garin Monguno domin gane wa kansa yadda aikin ginin babban asibitin garin ke tafiya.

SAURAI: Wa Ya Kamata Ya Jikan ’Yan Gudun Hijira?

Ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyi gudun hijira har zuwa kasashen waje daga jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe.

A lokacin ziyarar ta ranar Laraba, Gwamna Zulum ya kira rajistar ma’aiakatan asibitin, sannan ya sa a dakatar da albashin jami’an lafiyan da suka yi fashin aiki, a kuma kara na wadanda ya samu a bakin aikinsu albashi nan take.

“Duk ma’aikatan lafiyan da suka cancanta za su samu karin kashi na albashinsu daga yanzu zuwa shekara daya mai zuwa, lokacin da ake sa ran ta’addanci ya kau,” inji shi.

Gwamnan ya yi alkawarin daukar karin ma’aikata a Babban Asibitin na Monguno da kuma kuma gina gidaje 15 domin ma’aikata.

Ya kara da cewa za a kawo duk kayan aiki da magungunan da ake bukata a asibitin cikin mako guda.

Tun da farko Babban Jami’in Kula da Asibitn, Isa Akinbode, ya koka wa gwamnan kan karacin ma’aikata da kuma rashin dakin yin gwaje-gwaje.

Da ya kai ziyarar ba-zata a wata makarantar sakandaren da ke garin, malamai sun yi masa korafi cewa baya ga karancin malamai, makarantar na fama da rashin kujeru da kuma katanga saboda tsaro.

A nan ma Zulum ya yi alkawarin daukar karin malamai, sannan ya ce za a matsar da ’yan gudun hijira da ke zaune a kusa da makarantar domin kauce wa yin kutse a filin makarantar.