✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kebe wa mutanen da ba Umrah suke ba lokacin sumbatar Hajarul Aswad

Za a ware musu lokacin shiga Hijir da kuma taba Ruknun Yamani.

Masallacin Harami zai fara ba da izinin ci gaba da yin Dawafi da kuma sumbatar ‘Hajarul Aswad’ ga mutanen da ba sa gudanar da ibadar Umrah.

A makon gobe ake sa ran fara bayar da izinin yin shiga harabar Dakin Ka’aba (Hateem) domin yin Dawafi da sumbatar Hajarul Aswad da Sallah a cikin Hijir da kuma taba Ruknin Yamani ga mutanen da ba Umrah suke yi ba.

Jaridar Saudi Gazette ta ambato majiyoyi masu tushe a Masallcin Harami na cewa za a sanya bangaren neman izini yin dawafin a manhajojin Tawakkalna da Eatmarna domin masu son yin dawafi a cikin Hateem.

Kwamandan Runduna ta Musamman da ke samar da tsaro a Masallacin Harami, Muhammad Al-Bassami, ya ce za a keba hawan farko na ginin Masallacin Harami domin mutanen da ba Umrah suke yi ba, su yi Dawafi.

Hakan ya zo daidai da umarnin Sarki Salman na Saudiyya kuma Hadimin Masallatai Masu Alfarma, na bayar da dama ga masu ibada su ci moriyar kowace dama ta yin ibada a masallacin.

Hijir wani bangare ne na dakin Ka’abah, amma a halin yanzu yana bude an yi masa wata gajeruwar katanga, sai lokaci zuwa lokaci ake bari mutane su shiga ciki.

Yana daga cikin wuraren da ake karbar addu’a, shi ya sa a kowane lokaci masu Dawafi ke rige-rige da turmutsutsin shiga su yi Sallah da addu’o’i. Kusurwar da ke gaba da na kofar Hijir a jikin dakin Ka’aba shi ne Ruknin Yamani, wanda daga shi sai kusurwar Hajarul Aswad.

A watan Ramadan din da ya gabata ne aka dakatar da mutanen da ba sa Umrah yin dawafi, gami da hana masu Umrah taba Dakin Ka’aba a Masallacin Haram, a matsayin matakin kariyar cutar COVID-19.