✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kwace filayen da masu su suka ki ginawa a Abuja

Ya kuma ce hukumar za ta fara kwace filayen da aka raba wa masu harkar gine-gine.

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta ce ta shirya tsaf domin kwace dukkan filayen da masu su suka yi kunnen uwar shegu da umarninta na gina su.

Darakta Sashen Tattara Bayanai na Hukumar Tsara Birane ta a birnin, Alhaji Muhammad Sule ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata a Abuja.

Ya kuma ce hukumar za ta fara kwace filayen da aka raba wa masu harkar gine-gine da dama da nufin gina rukunin gidaje amma suka ki amfani da su.

Daraktan ya ce daukar matakin ya zama wajibi kasancewar gwamnati ta kashe makudan kudade wajen samar da kayayyakin more rayuwa kuma ba za ta barsu su tafi a banza ba.

Alhaji Muhammad ya ce tuni hukumar ta kammala tattara bayanai kan wadanda suka gina da kuma wadanda basu gina ba kuma ta himmatu wajen kwace su da nufin sake bayar da su ga wadanda za su gina.

Ya ce tsawon lokaci an bayar da irin wadannan filayen domin gine-gine daban-daban na gidajen kwana, wuraren kasuwanci da kuma rukunin gidaje.

Ya ce, “Rashin ginawar ta sa sun hana dubban masu sha’awar mallakar gidaje a Abuja yin hakan.

“Akwai bukatar mu tunatar da wadannan mutanen su yi abin da ya kamata. Abin takaici ne matuka yadda wasu daga cikinsu suka ki amfani da umarninmu,” inji shi.

Ya ce tuni hukumar ta wayar da kan jama’a ta kafafen watsa labarai da dama a kan hakan domin su dauki matakin amma suka yi shakulatin-bangaro da ita.