Za a kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Saudiyya | Aminiya

Za a kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Saudiyya

    Abubakar Muhammad Usman

Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawar diflomasiyya tsakaninta da Gwamnatin Kasar Saudiyya don kwaso ‘yan Najeriya wadanda wa’adin takardun izinin zamansu a kasar ya kare.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da hakan cikin birnin Abuja a ranar Litinin yayin gabatar da jawaban karin haske dangane da halin annobar Coronavirus a kasar.

Ya ce, “Yanzu haka muna tattaunawa da masarautar kasar Saudiyya, don kwaso ‘yan Najeriya 600 da suka makale a kasar.”

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin ya fitar ta bayyana cewa za a kwaso ‘yan Najeriyar cikin kwanaki biyu daga ranar 28 zuwa 29 ga Janairu.

Ya kara da cewa, da zarar sun dawo za a killace su na tsawon mako biyu kamar yadda ka’idodin dakile yaduwar cutar Coronavirus suka tanadar.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, gwamnatin Saudiyya ta kama ‘yan Najeriyar ne wadanda wa’adin takardun izinin zamansu a kasar ya kare.