✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a maida gidajen kallo makarantun Islamiyya a Katsina

Da wannan mataki zai sa a san addinin sannan kuma ilmantu.

A makon nan ne ’yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina suka tattauna yiwuwar maida duk wuraren kallo da gwamnati ta gina a kauyuka da garuruwan jihar zuwa makarantun Islamiyya.

Dan Majalisar da ke wakiltar Karamar Hukumar Jibia, Mustapha Yusuf ne ya jagoranci muhawarar a zauren Majalisar yayin zamanta na ranar Talata.

“Lokaci ya yi da za a maida gidajen kallon Talbijin da aka gina a kauyukan su koma makarantun Islamiyya domin sune ake bukata yanzu ba wuraren kallce-kallce ba.

“Na yi hira da wasu ’yan bindiga kuma koken da suka yi min kenan na rashin makarantu da suke fama da su.

“Sannan kuma su kansu wuraren kallo da yawa daga cikin su sun zama kufayi, sun lalace.

“Idan majalisa ta amince da wannan kudirin za a samu saukin Almajirai dake gararamba a jihar.

“Haka kuma za a debi malamai wanda za su rika karantar da yara, shi ma hakan hanyar samar da aikin yi ne.

“Tarbiyya ta tabarbare saboda rashin ilimin addini da ya yi karanci a tsakanin yara.

“Amma da wannan mataki zai sa su san addinin su sannan su kuma ilmantu.

“Wasu daga cikin gidaden kallon sun zama matattaran miyagu da ’yan iska,”a cewarsa.

A karshe Kakakin Majalisar, Tasi’u Maigari ya mika kudirin ga Kwamitin Addini domin su duba sannan su bai wa majalisar shawara kan abinda ya kamata su yi.

Jihar Katsina, kamar wasu jihohin Arewa Maso Yamma, na fama da matsalar tsaro inda hare-haren ’yan bindiga ya yi tsanani  gami da sace dalibai a makarantu.