✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a raba gardama a wasan karshe na Gasar Firimiyar Ingila

Sai a wasan karshe za a raba gardama tsakanin Manchester City da Liverpool.

Liverpool ta kara wa Manchester City matsin lamba bayan ta doke Southampton da 2 – 1 a Gasar Firimiyar Ingila a daren ranar Talata.

Nasarar Liverpool ta sa sai a wasan karshe za a san kungiyar da za ta lashe gasar tsakanin Manchester City da Liverpool.

Joel Matip ne ya zura wa Liverpool kwallo ta biyu a raga da ta ba ta nasarar kara matsa wa Manchester City lamba.

Idan har Liverpool ta samu nasara wajen lashe gasar Firimiya a bana, hakan na nufin ta lashe gasar sau biyu cikin shekara 32.

Sai dai a wasan karshe Liverpool za ta kara da Aston Villa, kungiyar da tsohon kyaftin dinta, Steven Gerrard, yake horaswa.

Jurgen Klopp ya yi sauye-sauye a wasansu da Southampton, inda ya bai wa manyan ’yan wasansa da dama hutu, duba da karatowar wasan karshe na Gasar Zakarun Turai, inda za ta kara da Real Madrid.

Yanzu Manchester City ce ke jan ragamar gasar da maki 90 daga wasanni 37, sai Liverpool a matsayi na biyu da maki 89 daga wasanni 37.