✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a raba gidan sauro miliyan 2 a Gombe

Za a raba gida sauron sama da miliyan biyu don amfanin jama'ar jihar.

A kokarin gwamnatin Jihar Gombe da hadin gwiwar shirin Gwamnatin Tarayya na National Malaria Elimination program da tallafin Asusun Duniya na Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, za su raba gidan sauro mai dauke da magani guda 2,328,346 a jihar.

Za a raba gidajen sauron ne ta hanyar bin gida-gida ana daukar bayanan magidanta ana raba musu don tabbatar da kowanne uwargida ta samu gidan sauro a gangamin yaki da ake yi na kawar da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya.

Batun hakan ya fito ne ta bakin jami’ar gwamnatin tarayya a bangaren yaki da zazzabin cizon sauro Misis Hope Obokoh.

Obokoh ta yi jawabin ne a Jihar Gombe a lokacin taron wayar da kai da suka shirya wa ‘yan jarida don fadakar da al’ummar gari muhimmanci amfani da gidan sauro mai dauke da magani.

Misis Hope Obokoh, ta ce za a rarraba gidan sauron ne a Kananan Hukumomi 11 na Jihar a cikin kwanaki 12, inda za a fara daga ranar 3 zuwa 14 ga watan Satumba mai zuwa.

A cewarta idan aka bawa mutum gidan sauron ya shanya shi a inuwa na tsawon sa’a 24 kafin ya fara kwana a cikinsa, kuma ba shi da wata illa.

A wata makala da Misis Nneka Ndubuisi ta gabatar, ta ce fatansu shi ne a samu kashi 80 cikin 100 idan ba a samu 100 bisa 100 ba na wadanda za su samu gidan sauron.

Ndubuisi, ta kara da cewa rabon gidan sauron a kan yi shi duk bayan shekara uku zuwa hudu.

Ta ce Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince mutum biyu su kwana a cikin kowane gidan sauro guda daya.

Kazalika, ta ce ya zuwa an rarraba kimanin gidan sauro miliyan 20 a fadin Najeriya.

Shi ma wakilin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Mista Philip Okoko, cewa ya yi sun zabo ‘yan jarida ne don su taya su wannan gangami ta hanyar ilmantar da al’umma muhimmancin amfani da gidan sauron.

Okoko ya kara da cewa, a duniya cikin kowane mutum hudu da ke kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ana samun mutum guda daya daga Najeriya.

Kuma duk cikin kowacce sa’a mutum biyu ke mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro a Najeriya.

A cewarsa, ta hanyar amfani da gidan sauro mai dauke da magani ne kadai za a iya shawo kan matsalar.

Haka kuma, ya ce ba a cika amfani da gidan sauro a Najeriya ba saboda rashin sanin muhimmancinsa, lamarin da ya sanya suka shigo da ‘yan jarida cikin gangamin domin wayar da kan al’umma.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa reshen Jihar Gombe, Kwamred Sa’idu Bappah Malala, ya yi godiya ga bangarorin da suka shirya taron.

Ya yaba musu dangane da yadda suka shigar da ‘yan jarida ciki kuma ya tabbatar musu da cewa ‘yan jarida abokan aiki ne da za su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sakon ya isa inda ake bukata.