✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rantsar da sabbin alkalan kotunan Musulunci 34 a Kano

Babban Alkalin Jihar Kano, Mai Shari'a Nura Sagir, ya amince da nadin karin alkalai kotunan Musulunci.

Babban Alkalin Jihar Kano, Mai Shari’a Nura Sagir, ya amince da nadin karin alkalai 34 a kotunan Musulunci da ke Jihar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’ar Jihar Kano, Baba Jibo-Ibrahim, ya ce Babban Alkalin ya amince da nadin alkalan ne bayan sun ci jarabawar da Hukumar Kula Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta gudanar.

Game da rantsar da alkalan, ya ce, “Ana bukatar sabbin Alkalan Kotunan Shari’ar Musuluncin da za a rantsar ranar Juma’a 25 ga watan Yuni 2021 da su hallara a Babbar Kotu da misalin karfe 10.00 na safe.”

Ya bayyana hakan ne a sanarwar da ya fitar a safiyar Alhamis wadda ke tababtar da nadin sabbin alkalan.