✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rufe gidajen abincin da ba su yi gwajin lafiya ba a Kano

An samu ma'aikatan gidajen sayar da abinci da ciwon hanta.

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani wurin sayar da abinci bayan da aka gano ma’aikatansu na dauke da cutar hanta mai kisa.

Hukumar Kare Masu Sayayya ta jihar ta ce bayan gudanar da gwaji ne aka gano ma’aikatan na dauke da cutar hanta, kuma nan take aka ba da umarnin rufe wuraren har zuwa lokacin da za su samu lafiya.

Ta kuma ba da umarnin rufe duk gidajen abinci, gidaje burodi, da kamfanonin sana’anta ruwa, marasa rajista da Ma’aikatar Lafiya ta jihar.

Hakan na zuwa ne bayan cikar wa’adin da gwamnatin ta bayar ta hannun Hukumar, kamar yadda Shugaban Hukumar, Baffa Babba DanAgundi ya bayyana a ranar Alhamis.

Baffa, ya ce dole ne kowane gidan abinci, a tabbatar da lafiyarsa, bayan an samu wasu wuraren sayar da abinci da ma’aikatansu ke dauke da cutar hanta mai kisa.

Ya ce wannan matakin yin zagaye a wuraren sayar da abinci ya zama wajabi don kare lafiyar al’ummar jihar daga kamuwa da cututtuka barkatai.