✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rufe kasuwar Wuse da ke Abuja saboda karya dokar COVID-19

Za a rufe kasuwar da wasu manyan shaguna ranar Talata bayan kotu ta kama su da laifi.

Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya za ta rufe Kasuwar Wuse da ke Abuja a ranar Talata saboda saba dokokin takaita yaduwar cutar COVID-19.

Jami’in Wayar da Kan Jama’a na Kwamitin Yaki da COVID-19 da Ministan Abuja ya kafa, Iharo Attah, ya ce kwamitin zai kuma rufe Cibiyar Cinikayya  UTC da kuma Morg Plaza dakkanninsu a yankin Area 10 a Abuja.

Ya bayyana haka ne bayan Mai Shari’a Idayat Akanni ta yanke hukunci tare da bayar da umarnin a zaman Koutun Majistaren ta tafi-da-gidanka a ranar Litinin.

Jami’in ya ce hukuncin kotun ya zo daidai da dokar da Shugaban Buhari ya sanya wa hannu kan hukunta masu karya dokar cutar.

An kuma gurfanar da kusan mutum 100 a gaban kotun saboda karya dokokokin hana yaduwar cutar COVID-19, musamman rashin sanya takunkumi.