✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rufe shafukan batsa a Faransa

Kasar na neman umarnin kotu na toshe duk hanyoyin shiga wasu shafukan batsa a kasar, kai-tsaye ko ta bayan fage

Gwamnatin Faransa na shirin tsohe wasu manyan shafukan yada batsa na intanet guda biyar a kasarta.

A ranar Talata, Gwamnatin Faransa ta sanar cewa ta shigar da karar shafukan Pornhub, Tukif, Xhamster, Xnxx da kuma Xvideos, wadanda suka yi kaurin suna a duniya wajen yada hotuna da bidiyon batsa ta intanet.

Shugaban hukumar da ke kula da kafafen yada labarai a Faransa, Arcom, Mista Roch-Olivier Maistre, ya ce, “Idan an yi mana adalci, za a toshe duk hanyoyin shiga wadannan shafukan batsa a kasar nan kai-tsaye ko ta bayan fage.”

Gwamnatin ta bayyana cewa tana sa ran samun umarnin kotu na toshe ayyukan kafofin na yada badala gaba daya a kasar, saboda sun yi buris da umarninta tun a 2021 na cewa su daina barin kananan yara masu kasa da shekara 18 ziyartar shafukansu.

Umarnin gwamnatin, wadda ta yi doka a kansa a watan Yulin 2021, ya ce tambayar mai ziyartar shafin intanet ko shekarunsa sun haura 18 kadai bai wadatar ba.

Wajibi ne masu shafukan intanet su bullo da wata hanya da za ta tabbatar da hana kananan yara kallon batsa ta shafukansu.

Pornhub dai shi ne kafar yada batsa mafi girma a duniya.

A watan Disamban 2021, shadin Tukif, mai mazauni a kasar Portugal ya shigar da kara yana zargin nuna mishi wariya saboda karar da gwamantin ta shigar ba ta shafi wasu shafukan batsa na cikin gida a kasar ba.