✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za a sami ambaliyar ruwa a Kananan Hukumomi 233 na Najeriya’

Akwai yiwuwar samun matsalar a Jihohi 32 da Abuja a bana

Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta ce harsashe ya nuna yiwuwar samun ambaliyar ruwa a Kananan Hukumomi 233 da ke Jihohi 32 da Babban Birnin Tarayya Abuja a daminar bana.

Shugaban Hukumar, Clement Nze ne ya sanar da hakan yayin wani taron gabatar da rahoton annobar da za a iya fuskanta a shekarar 2022, wanda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a Abuja ranar Asabar.

A cewar shi, daga cikin Jihohin da suka fi tabbacin yiwuwar samun ambaliyar ruwan akwai Gombe da Imo da Jigawa da Kaduna da Kano da Kebbi da Kogi da Kwara da Legas da kuma Nasarawa.

Sauran sun hada da Neja da Ogun da Ondo da Oyo da Ribas da Sakkwato da Taraba da Gombe da Zamfara da kuma Abuja.

Clement ya kuma ce a Kananan Hukumomi 212 da ke Jihohi 35 da Abuja, akwai yiwuwar samun matsakaiciyar ambaliyar.

Shugaban hukumar ya ce ragowar Kananan Hukumomi 329 kuwa suna cikin wadanda ba lallai ne a fuskanci ambaliyar a cikinsu ba.

Ya ce ana harsashen fuskantar ambaliyar mai karfi a Kananan Hukumomi 57 a watannin Afrilu da Mayu da kuma Yuni, yayin da a wani bangare na Kananan Hukumomi 220 za a samu ambaliyar a watannin Yuli da Agusta da Satumba.

A nashi jawabin, Shugaban hukumar NEMA, Alhaji Mustapha Habib Ahmed, ya ce ya zama wajibi ga daidaikun mutane da gwamnatocin jihohi su dauki ragamar magance matsalar ambaliyar, maimakon su kyale komai a hannun Gwamnatin Tarayya.

Matsalar ambaliyar ruwa dai ta zama wata babban kalubalen muhalli da yanayi da ake fuskanta kowacce shekara a Najeriya, inda take haifar da asarar rayuka da dukiyoyi a sassan kasar daban-daban.