✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a samu karancin wutar lantarki ranar Laraba —TCN

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kasa (TCN), ya ce za a samu karancin wutar lantarki da megawatt 50MW ya zuwa ranar Larabar ta wannan makon.…

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kasa (TCN), ya ce za a samu karancin wutar lantarki da megawatt 50MW ya zuwa ranar Larabar ta wannan makon.

Sanarwar da TCN ya fitar a ranar Litinin ya ce karancin wutar zai auku ne sakamakon aikin gyaran da ya saba yi duk shekara a tashar wuta ta Lekki, Jihar Legas.

Kamfanin ya ce a yayin gudanar da aikin, za a samu raguwar wutar lantarkin da 50MW wanda zai shafi yankunan Lekki phase 1 da Oniru da Elegushi da Waterfront da Igbo Efon da kuma rukunin gidajen Twenty-first Century, duk a Jihar Legas.

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ba da tabbacin samar da megawat 5000MW na wuta ga ’yan Najeriya daga ranar 1 ga watan Yulin da ake ciki.

Karancin lantarki na daga cikin manyan matsalolin da suka yi wa Najeriya dabaibayi.

Ko a wannan shekarar an samu daukewarta daga cibiyar lantarki ta kasa sau da dama.

TCN dai ta ce tana iya bakin kokarinta don samar da wadatacciyar wutar ga ’yan Najeriya.