✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a soma bincike kan kone ‘barawon babur’ a Bauchi

Daukar doka a hannu dabbanci ne da rashin mutunta dan Adam.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Umar Sanda, ya ba da umarnin a gaggauta gudanar da bincike dangane da kone wani mutum da aka yi wanda aka zarga da satar babur a garin Chinade da ke Karamar Katagum a jihar.

Umarnin Kwamishinan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, SP Ahmed Wakili, wadda aka raba wa manema labarai a Bauchi.

Sanda ya bayyana mummunan hukuncin da fusatattun matasan suka dauka a kan wanda ake zargin a matsayin dabbanci da rashin mutunta dan Adam.

Ya ce, “Maimakon su kama wanda ake zargin su mika shi ga ‘yan sanda don gudanar da bincike da kuma hukunta shi, amma suka kona shi bisa zargin satar babur ba tare da la’akari da matsayin doka ba.”

Don haka jami’in ya ce, rundunar a karkashin jagorancinsa ba za ta zuba ido sannan ta kalli bata-gari na daukar doka a hannunsu ba a cikin al’umma, suna kashe wanda ake zargi da aikata laifi da saba wa doka.

Kwamishinan ya jaddada cewa babu wanda ke da ‘yancin kashe wanda ake zargi, yana mai gargadin masu daukar doka a hannu da suka shiga taitayinsu.

Ya bukaci duk wanda aka kama da zargin aikata wani laifi, a gaggauta mika shi ga ‘yan sanda ko hukumar da ta dace don gudanar da bincike.

Jami’in ya bukaci al’ummar yankin su kwantar da hankalinsu, tare da ba su tabbacin ‘yan sanda sun soma bincike kan lamarin don gano wadanda ke da hannu a lamarin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a Lahadin da ta gabata ce wasu fusatattun matasa suka yi wa marigayin jina-jina kana daga bisani suka kona shi duk saboda zargin satar babur.