✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a toshe layin sadarwa a Kaduna —El-Rufai

El-Rufai ya ce ’yan bindigar Zamfara da Katsina na gudowa zuwa Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta sanar da jama’ar jihar cewa su kasance cikin shiri domin za ta iya toshe layin sadarwa saboda sojoji za su kai hare-hare kan ’yan bindigar da ke gudowa daga wasu jihohi. 

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya riga ya nemi izinin Gwamnatin Tarayya kan rufe layukan sandarwar kuma ya samu amincewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

“Ina so mutanen Jihar Kaduna su sani cewa ko gobe (Laraba) sojoji suka ba mu tabbaci za mu iya rufe  layin sadarwa,” inji shi.

A hirarsa da gidajen rediyon jihar ranar Talata da dare,  gwamnan ya ce, “Babu shakka ’yan bindiga da sauran masu aikata manyan laifuka sun dogara ne da hanyar sadarwa wurin yin magana da masu basu bayanai da kuma dangin wadanda suka sace don neman kudin fansa”.

Sai dai El-Rufai ya ce toshe layukan sadarwar zai takaita ne a kananan hukumomi da ke da iyaka da jihohin Zamfara da Katsina inda sojoji ke zargargazar ’yan bindiga.

Gwamna El-Rufai ya ce rahotanni sun nuna cewa a sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa ’yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina inda aka rufe layukan sadarwa, ’yan bindiga kan tsallako zuwa wasu kananan hukumomin Jihar Kaduna da ke makwabtaka da su domin su kira waya su nemi kudin fansa.

Ya bayyana cewa: “Sojoji sun ba mu shawarar rufe layukan sadarwa a wasu kananan hukumomi, amma muna jira su bayyana mana kananan hukumomin da kuma lokacin.”

“Ba zan bayyana sunayen kananan hukumomin ba, amma su kananan hukumomin da ’yan bindiga suka fi addaba sun san kansu.

“Amma da zarar hukumomin tsaro sun ba mu tabbaci, mutane su sani cewa za mu rufe layukan sadarwa don mu ba hukumoin tsaro cikakken hadin kai su gudanar da ayyukansu a yankunan.”

Kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kajuru da Kachia dai su ne wadanda ’yan bindiga suka fi addaba a Jihar Kaduna.

El-Rufai ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin aiki da cikawa na dabbaka matakan da ta dauka na rufe gidajen mai da kasuwanni a yankunan da ke makwabtaka da dazukan da ’yan bindiga ke zama.

Ya yi kira ga jama’a da su taimaka ta hanyar kai karar masu hada baki ko ba wa ’yan bindiga bayanai.

“Duk wanda aka gani zai sayi sinki burodi 20 ko fiye da hakan a sayar masa amma a sanar da hukumomin tsaro; Haka ma duk wanda ya kawo wayoyi da yawa yana neman a yi masa cajin su.