✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi gwanjon rigar Maradona kan fam miliyan 4

Ba ita ce rigar da mahaifina ya sanya ba a zango na biyu na wasan.

Rigar da Diego Maradona ya saka a lokacin da ya zura kwallo a ragar Ingila a gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 1986, ana sa ran za a sayar da ita a kan akalla fam miliyan 4.

Kwallon wadda Maradona ya jefa a wasan ta hanyar amfani da hannunsa tsawon shekaru 36 da suka gabata, ta shiga tarihi da ake yi mata lakabi da ‘The Hand of God’.

Rigar dai a yanzu mallakin tsohon dan wasan tsakiya ce na Ingila Steve Hodge, wanda ya yi musayar riga da Maradona bayan da Argentina ta doke su da ci 2-1.

Kwallon da Maradona ya jefa a wasan Cin Kofin Duniya da Argentina ta fafata da Ingila a shekarar 1986

A kimanin shekaru biyu da suka gabata, bayan mutuwar Maradona a 2020, Hodge ya ce rigar gwarzon dan wasan ba ta siyarwa ba ce.

Maradona, wanda ya jagoranci Argentina zuwa nasarar lashe gasar cin Kofin Duniya a 1986, na daga cikin manyan gwarazan ‘yan wasa a tarihin kwallon kafa, ya mutu yana da shekaru 60 sakamakon bugun zuciya.

Sai dai a yanzu an shiga rudani kan ainihin rigar da ake batun yin gwanjonta, inda diyar marigayin, Dalma da kuma tsohuwar matarsa, Claudia Villafane suka yi ikirarin cewa ba ita ce rigar da ya sanya ba a wasan da aka fafata a kasar Mexico bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Iyalan mamacin sun bayyana cewa rigar tana hannun wani mutum na daban ba Steve Hodge da ake ikirari ba.

Dalma Maradona ta ce, “ba ita ce rigar da mahaifina ya sanya ba a zango na biyu na wasan.

“Ina da tabbacin cewa rigar ba ta hannun Hodge kuma na san wanda ya ke da ita, amma bana son na fada saboda babu lallai hankali ya dauka.”

Ana iya tuna cewa, rigar da gwarzon duniya na kasar Brazil Pele ya sanya a wasan karshe na gasar cin Kofin Duniya a shekarar 1970 ita ce rigar kwallon kafa mafi tsada da aka sayar da ita a gwanjo, a cewar littafin adana ababen tarihi na duniya wato ‘Guinness World Records’.

An yi gwanjon rigar ta Pele kan kudi fam miliyan 157 da dubu 750 a shekarar 2002.