✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi karon-batta tsakanin Chelsea da City a wasan karshe na kofin zakarun Turai

Kungiyoyin kwallon kafa biyu da ke murza leda a Ingila, Manchester City da Chelsea, sun samu nasarar yankar tikitin haduwa da juna a wasan karshen…

Kungiyoyin kwallon kafa biyu da ke murza leda a Ingila, Manchester City da Chelsea, sun samu nasarar yankar tikitin haduwa da juna a wasan karshen na gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana.

City da Chelsea za su yi karon-batta ne a filin wasa na Ataturk Olympic da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya bayan nasarar da suka samu ta doke abokan karawarsu a matakin daf da na karshe na gasar Turan.

Tun a daren Talatar da ta gabata ce Manchester City ta samu nasarar kai wa wasan karshen bayan ta yi PSG lilis a wasan da aka tashi ci 2-0 a Faransa.

Kazalika, ita ma Chelsea a daren Larabar da ta gabata ce ta saita wa Real Madrid hanyar komawa gida bayan ta yi mata duka a Stamford Bridge inda ta zira kwallaye biyu a haduwarsu ta biyu bayan ta farko da aka tashi 1-1 a matakin gab da na karshe na gasar.

Kamar yadda ta kasance a bara yayin haduwar Liverpool da Tottenham, kungiyoyin Ingila ne za su sake haduwa da junansu a wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai ta bana.