✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi wa Buhari da gwamnoni karin albashi

Shugaban RMAFC ya ce lokaci ya dade da yi na karin albashi ga masu rike da mukaman siyasa da dangoginsu.

Hukumar Tattarawa da Raba Kudin Shiga ta Kasa (RMAFC), ta ce ta kammala shirye-shiryenta don yin karin albashi ga Shugaban Kasa da mataimakinsa da gwamnoni sa mataimakansu.

Sauran sun hada da masu rike da mukaman siyasa da alkalai da wasu masu rike da mukaman gwamnati.

Shugaban RMAFC, Mohammed Bello Shehu ne ya ce lokaci ya dade da yi na karin albashi ga masu rike da mukaman siyasa da dangoginsu, saboda rabon da a yi hakan tun shekarar 2008.

Ya bayyana haka ne, yayin da ya ziyarci shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato a ofishinsa da ke Abuja.

Sai dai kuma, da alama yukurin RMAFC na yi wa ’yan siyasa da sauransu karin albashin bai yi wa Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) dadi ba.

Domin kuwa, kungiyar ta ce mafi karancin albashi na N30,000 da ake biyan ma’aikatan gwamnati bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da makudan kudaden da ake biyan ’yan siyasar kasar nan.

NLC ta ce ma’aikatan gwamnati a matakin kasa da jihohi da kananan hukumomi ne suka cancanci samun karin albashi, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen tattalin arziki gami da tsadar rayuwar da ake fuskanta.

Bello ya ce dokar kasa ce ta bai wa RMAFC ikon yanka albashin da za a rika biyan ’yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati da kuma ma’aikatan fannin shari’a.