✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Daga yanzu duk wanda zai ziyarci Aso Rock sai an masa gwajin COVID-19’

An fito da tsarin yin gwaji ga baki masu ziyartar fadar shugaban kasa.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabon tsari na yi wa baki masu ziyartar Fadar Shugaban Kasa, gwajin COVID-19 kafin ba su damar shiga fadar ta Aso Rock da ke Abuja.

Daga cikin wadanda za a rika yi wa gwajin sun hadar da baki na musamman da Gwamnoni da ke kai ziyara a ko da yaushe.

A cewar Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Kasa, ya zama tilas a yi wa duk wanda zai shiga fadar gwajin COVID-19.

Sai dai ya ce akwai shugabannin da aka ware musamman wanda suka shigo daga ketare, amma su ma ana shawartarsu da su yi gwajin cutar don tabbatar da lafiyarsu.

“Haka ne, an fito da sabuwar doka game da COVID-19 ga masu kawo ziyara Villa, ba wai a kan Gwamnoni kadai ba.

“Duk bakon da zai zo Villa, musamman wanda suka zo ganin Shugaban Kasa dole ne a musu gwaji kafin shiga.

“Gwajin kyauta ne, babu bukatar mutum ya biya wani abu, saboda an samar da kayan gwajin cutar. An dauki wannan mataki ne saboda yadda cutar ke ci gaba da bulla a tsakanin al’umma.

“Sai dai akwai wadanda aka ware ba za a yi wa gwajin ba, musamman wanda suka zo daga waje, amma su ma ana shawartarsu da su yi gwajin.

Matakin na zuwa ne bayan yadda mutane da dama a fadar suka kamu da COVID-19, ciki har da Malam Garba Shehun, wanda ya warke a makon da ya gabata.