✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu agaza wa Chadi kan zaman lafiya —Buhari

Buhari ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta taimaki Chadi don tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya za ta taimaka wa Chadi domin tabbatar da zaman lafiya da komawar kasar kan tafarkin dimokuradiyya.

Sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasa kan yada labarai Femi Adesina ya fitar jim kadan bayan ganawar shugabannin biyu ce ta bayyana haka.

“Kasashen biyu na da abubuwan da suka hada su, wato al’adu da kuma makwabtaka kuma Najeriya na sane da muhimmancin rawar da Chadi ta taka wajen yaki da ayyukan ta’addanci, sannan kasashen biyu za su ci gaba da wannan alaka a tsakaninsu,” cewar Adesina.

Buhari, ya ce Najeriya za ta taimaka wa Chadi domin tabbatar da zaman lafiya da kuma komawar kasar kan tsarin doka da oda.

Ya yi alkawarin ne a ranar Juma’a lokacin da ya gana da Shugaban Majalisar Riko Kwarya ta Chadi, Laftanar-Janar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya ziyarce shi a Abuja.

Ya bayyana tsohon Shugaba Marshal Idriss Deby Itno a matsayin “Amini kuma cikakken aboki ga Najeriya da ba za a taba mantawa da irin rawar da ya taka don kare Najeriya ba.’’

Sanarwar ta kara da cewa Buhari zai ba da gudunmuwar da ta dace don karfafa Hukumar Raya Tafkin Chadi (LCBC) da kuma jaddada goyon baya ga rundanar hadin gwiwar kasashen yankin.