✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu binciki malamin da ya daki dalibarsa da gora —Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamiti domin binciken zargin mummunar dukan da wani malami ya yi wa wata daliba duka da gora har ya yi…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken zargin wani malami da ya yi wa dalibarsa duka da gora har ya yi mata lahani a wuya da bayanta, a Makarantar Rochas Foundation da ke Zariya.

Kwamishinar Walwala da Bunkasa Al’umma ta Jihar Kaduna, Hafsat Baba, ta shaida wa Aminiya cewa kwamitin ya kunshi ita kanta da takwarorinta na ma’aikatun lafiya da shari’a da kuma ilimi, kuma za su fara gudanar da binciken ne ranar 1 ga watan Agusta.

Ta kara da cewa kwamitin zai gabatar da rahoton binciken da kuma shawarwari ga Gwamna Nasir El-Rufai bayan kammala aikinsa.

A cewarta, duk kudin da mahaifin dalibar, Malam Salihu Umar, ya kashe wajen nema mata magani Gwamnatin Jihar Kaduna za ta maida mishi.

Ta kuma nuna rashin jin dadinta bisa halin da makarantar Rochas Foundation ta nuna na kin amsa gayyatar da Cibiyar Kula da Cin Zarafin Kananan Yara da ke Zariya ta aike mata.

Tun farko Aminiya ta ba da labarin cewa daliba Hauwa Salihu, wadda ke aji biyu na babbar sakandare a makarantar ta Sami mummunar rauni a bayan wuyanta da kashin bayanta sakamakon mummunar dukan da wani malamin lissafin ya yi mata.

Mahaifin dalibar, Malam Salihu Umar ya ce har yanzu Hauwa tana ci gaba da jinya duk kuwa da cewa an sallame ta daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.