✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu biya ma’aurata Dala 3,000 su jaraba katifarmu

Wani gurbin aiki mai tsoka da aka ware wa ma’aurata kadai na ci gaba da daukar hankali. Cibiyar SleepStandard, mai rajin samar da lafiyayyen barci…

Wani gurbin aiki mai tsoka da aka ware wa ma’aurata kadai na ci gaba da daukar hankali.

Cibiyar SleepStandard, mai rajin samar da lafiyayyen barci ta fito da gasar katifun ma’aurata domin gano wadda ta fi inganci.

Shugaban SleepStandard, Chris Norris, ya ce za a ba wa ma’aurata sabuwar katifa a duk mako domin su zabi wadda ta fi musu dadi.

Wadanda suka zama zakaru za su samu kyautar Dala 3,000 (kimanin Naira miliyan daya da dubu dari biyar).

Ranar Ma’aurata ta 2020

An bullo da gasar ce domin zagayowar Ranar Ma’aurata ta 2020.

Ya ce suna ba wa marasa aure hakuri, amma ga ma’aurata  kuma wannan albishir ne.

Ana neman iyalai biyar kacal da za su shiga gasar katifun da aka shirya.

A duk mako za a tura musu sabbin katifu har gida su yi amfani da su.

Abun da ake bukata shi ne su bayyana wadda ta fi inganci wajen kwanciyar aure.

Za a ba iyalan da suka zama zakaru kyautar $3,000 (kimanin Naira miliyan daya da dubu dari biyar).

Dalilin bullo da gasar katifu

An bullo da gasar katifun ma’auratan ne domin magance cikas din da katifu marasa inganci kan kawo wa iyalai a lokacin kwanciyar aure.

Manufar ita ce gano katifar ma’aurata mafi inganci domin ba wa iyalai damar jin dadin lokacinsu.

Yadda abun yake

An bullo da ita ce domin murnar zagayowar Ranar Ma’aurata da ake yi a kowace 18 ga Agusta domin nuna kauna da tarairayar juna tsakanin ma’aurata.

Gasar na son ma’aurata biyar su taimaka a gano katifar da ta fi dacewa da kwanciyar aure.

Ma’auratan za su yi haka ne ta hanyar gwada katifu biyar a duk mako.

Za a ba wa kowadanne sabuwar katifa su “more lokacinsu”. Za su yi gwajin ne cikin sirri a gidajensu.

Wadanda suka yi nasarar shiga na da zabin bayyana kansu ko su kasance a sirrance. Duk yadda suka zaba daidai ne.

Yadda tsarin gwajin yake

Za a yi mako takwas ana gwajin katifun, saboda haka iyalan za su gwada katifu takwas-takwas.

Duk mako za a aika musu da sabuwar katifa kuma duk sadda aka kawo sabuwa za a karbi wadda aka ba su kafin ita.

Katifun da za a yi gasar da su su ne nau’ika takwas da ake gani a matsayin zabin ma’aurata.

Kowane mako ma’auratan za su gwada katifu biyar ke nan.

Ana bukatatar su yi bayani na gaskiya a kan yanayin kowace katifa.

Sannan za su ba wa kowacce maki daga 1 zuwa 10 ta bangarori kamar haka:

  • Tashi
  • Kara
  • Karfi
  • Karkon kusurwa
  • Nutsuwa
  • Hucewa
  • Jimilla
Kyautar da za su samu

Bayan sun yi abun da suka saba yi a lokacin nishadinsu, iyalan da suka yi nasara za su samu kyautar tsabar kudi Dala 3,000 da kuma sabuwar katifa da suka zaba.

Wurin da za a yi gasar

Saboda yanayin gasar, kowadanne ma’aurata za su yi gwajin ne a gidajensu ba tare da masu sa ido ko lura ba.

Za a kawo musu katifun da za su yi gwajin da su ne har gida.

Yadda za a shiga gasar

Dole masu neman shiga gasar su kasance sun haura shekara 18 da haihuwa.

Sannan su aika da kananan hotuna na fasfo.

Ko kuma gajeren bidiyo na minti ɗaya wanda a ciki suke bayyana sha’awar shiga gasar.

Ko kuma adireshinsu na shafukan zumunta.

Sai kuma sauran sharudda.