✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu ci gaba da taimaka wa Ukraine da makamai – NATO

Ya kuma ce suna fatan samun karin makaman nan ba da jimawa ba

Sakatare-Janar na Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya yaba wa Kasashen Yamma da sauran kawayen Ukraine kan tallafin makaman da suke ba ta a yakinta da Rasha.

Ya kuma ce suna fatan samun karin makaman nan ba da jimawa ba.

Shugaban ya yi kalaman ne a ranar Lahadi, kwana daya bayan Rasha ta yi ruwan hare-hare a kan wasu muhimman gine-ginen kasar.

A yayin hare-haren dai, Rasha ta halaka akalla mutum 30 a gidajen mutane da ke birnin Dnirpo na Ukraine.

“Alkawuran da ake yi a kwanan nan na samar da manyan makamai suna da muhimmanci, kuma muna sa ran hakan ta karu a nan gaba,” in ji Stoltenberg, gabanin tattaunawarsa da manyan hafsoshin tsaron kasashen.

Da aka tambaye shi ko kasar Jamus za ta bi sahu wajen samar da makamai ga Ukraine, sai ya ce, “Muna cikin wani mataki mai muhimmanci a wannan yakin. Muna fuskantar tsananin barazana, saboda haka yana da matukar muhimmanci mu tallafa wa Ukraine da makamai.

Ko a ranar Asabar, sai da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy ya kira kasashen Yamma da su dada taimaka musu da karin makamai domin su tunkari abin da ya kira da ‘ta’addancin Rasha’ a kasarsa.