✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yajin aikin ASUU —Buhari

An bukaci a sake duba matsayin gwamnati na idan ba ka yi aiki ba babu albashi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ganin an kawo karshen tankiyar da ta ki ci ta ki cinyewa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.

Buhari ya dauki wannan kudirin ne yayin ganawa da shugaba da wasu zababbun mambobin kwamitin shugabannin gudanarwar jami’o’in tarayya kan batun yajin aikin kungiyar malaman.

Mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Farfesa Nimi Briggs, shi ne ya jagoranci zaman wanda ya ce sun yi da nufin ganawa da shugaban kasa a matsayinsa na shugaba kuma babban kwamandan sojin kasar, a matsayin uban kasa, kuma a matsayin mai ziyartar jami’o’in gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa, duk da rashin jin dadin da yajin aikin na sama da wata bakwai ya haddasa, “makomar jami’o’in kasar na da armashi,” har ya ba da misali da jami’ar Ibadan da ta shiga jerin sunayen jami’o’i 1,000 masu kyau a duniya, wani ci gaba da aka gani a karon farko.

Farfesa Briggs ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa amincewar da ta yi da wasu bukatun malaman da ke yajin aiki, ciki har da bukatar karin albashin bai daya na kashi 23.5 cikin 100, da kuma karin albashin Farfesoshi da kashi 35 cikin 100.

Ko da yake, Farfesa Briggs ya nemi a dan kara albashin la’akari da yayanin tattalin arzikin kasar.

Shugabannin gudanarwar jami’o’in sun kuma bukaci a sake duba matsayin gwamnati na “idan ba ka yi aiki ba babu albashi,” yayin da suka yi alkawarin cewa malamai za su yi aiki don cike gibin da aka samu tsawon lokacin yajin aikin da zarar an cimma matsaya, an kuma bude makarantu.

Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Nana Opiah, ya ce duk abubuwan da Gwamnatin Tarayya ta cimma matsaya a kansu don ganin an kawo karshen yajin aikin ne, amma kungiyar ASUU ta ki.