✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu daure masu kasuwanci a titin jirgin kasa —Amaechi

Za a kama a kuma daure masu kasa kaya da masu biyan bukata a kan titin jirgin kasa

Gwamnatin Tarayya za ta fara kamawa tana kuma hukunta mutanen da ke yin kasuwanci a kan titin jiragen kasa.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya sanar da haka a lokacin da yake bayyana damuwa kan karuwar masu karkasa kayan sayarwa ko biyan bukatunsu a kan titin jirgin kasa a Jihar Legas.

“Yadda mutane ke yin bayan gida da kuma karkasa hajoji a kan titin jirgin kasa a Legas abun damuwa ne. Hakan ya mayar da sabon titin jirgin kamar tsoho”, inji ministan.

Ya ci gaba da cewa, “Ni da Gwamantin Jihar Legas mun amince cewa titin jirgin kasa ba wurin ajiyar ababen hawa ba ne ko kasuwanci, saboda haka za a kama a kuma daure duk dan tiredan da ya kasa kaya a kan titin jirgin kasa; dole mu hana mutane yi wa titin jirgin kasa kutse a Legas”.

Da yake rangadin aikin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan mai nisan kilomita 156, Amaechi ya bayar da tabbacin cewa kamfanin CCECC na kasar China da ke gudanar da aikin zai kammala tashoshin jirgin kasa guda uku kafin karshen watan Satumba.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin mun kawo muku rahoton hatsarin jirgin kasa a Jihar Legas, wanda ya yi sanadiyyar asarar rai.

“Hatsarin da aka samu a baya-bayan nan ya faru ne saboda an ajiye motar a kan titin jirgin kasa. Masana sun shaida mini cewa jirgin kasa kan dauki mita 800 yana tafiya kafin ya tsaya idan ya taho a guje.

“An ajiye motar a wurin ne saboda mutanen da ke cikinta na jiran a bude babban shagon kasuwanci na Arena Shopping Complex.

Kasancewar sai jirgin ya yi tafiyar mita 800 kafin ya tsaya idan ya taho guje ta sa direban ba zai iya tsayawa cik ba saboda a kan hanyar titin jirgin aka ajiye motar.

“Shi ya sa jirgin ya kade motar wanda kuma hakan ya yi sanadiyyar asarar rai”, kamar yadda ya ce.