✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu fitar da sakamakon zabe a kan lokaci —INEC

INEC ta ba wa ’yan Najeriya tabbacin samun sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan Majalisun Tarayya a kan kari.

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ba wa ’yan Najeriya tabbacin samun sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan Majalisun Tarayya da ke gudana a yau a kan kari.

Idan za a iya tunawa a shekarar 2019 sai da aka kwana biyu da kammala zaben shugaban kasa kafin INEC ta sanar da sakamakonsa.

ِAmma shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ba da tabbacin cewa a wannan karon hukumar za a fitar da sakamakon da wuri.

Game da fargabar cewa tsarin sauyin kudi na Babban Bankin Najeirya (CBN) zai kawo wa cikas wajen gudanar da zaben 2023, shugaban hukumar ya ce kawo yanzu ba su da wata matsala ta wannan bangaren.