✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu gabatar da tafsirai cikin yaruka daban-daban a Gombe —JIBWIS

Za mu mayar da hankali wajen dasa akida a zukatan al’umma da karantar da sunnar Manzon Allah (S.A.W.)

Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’ikamatussunnah (JIBWIS) na Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe, ya ce kungiyar za ta gabatar da tafsirin Alkur’ani cikin yarukan da ake fahimta a Jihar domin amfanar al’umma.

Injiniya Salisu Gombe, ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da sunayen Malaman da za su gabatar da tafsiri a fadin Jihar da ma wasu sassan Jihar Borno a bana ga shugabanni da mambobin kungiyar a Sakatariyar JIBWIS da ke Bolari.

Ya ce dalilin da za a gabatar da Tafsirin cikin Yaruka daban daban shi ne don sakon ya isar wa wadanda ake tafsirin domin su, sannan ya ja hankalin Malaman da cewa su zurfafa bincike gabanin karantar da al’umma.

“ Yace ya zama wajibi mai tafsiri ya mayar da hankali a kan kyawawan dabi’u da mu’amala mai kyau da mutanen da zai zauna da su” inji Salisu.

Sannan ya kara da cewa mai gabatar da tafsiri ya gujewa kissa marar asali a Alkur’ani da kuma duk wani abu da shari’a ba ta yarda da shi ba, inda ya nemi da su fi mayar da hankali wajen karantar da al’umma abin da ya tabbata daga sunnah.

Ya ce, tafsirin zai mayar da hankali a kan manufofin kungiyar na dasa akida a zukatan al’umma da karantar da su sunna ta Manzon Allah (S.A.W.)

Ya kuma hori Malaman da su gujewa fatawa wacce za ta kawo rikici a tsakanin al’umma da sakin baki sakaka, inda a karshi ya karbi shawarwari daga mahalarta taron a kan abubuwan da aka tattauna.