✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu harba makaman nukiliya idan bukatar hakan ta taso —Rasha

Yakin Duniya na III zai kasance yakin da za a yi amfani da makaman nukiliya.

Ministan Harkokin Wajen Rasha ya yi gargadin cewa matukar Yakin Duniya na III ya barke, to ko shakka babu zai kasance yakin da za a yi amfani da makaman nukiliya akan juna.

To sai dai Sergei Lavrov ya ce idan har hakan ta faru, ba wanda za a zarga face kasashen Yammacin duniya.

“Wannan zance da ya shafi yin amfani da makaman nukilya, ba wanda ya fara yin sa face Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, har ma yana jan hankalin shugaba Vladimir Putin cewa, ya kamata ya sani ita ma Faransa ta mallaki irin wadannan makamai,” inji Lavrov.

Ministan ya kara da cewa, Zelensky ya yi irin wannan ikirari, yayin da shi kuma Stoltenberg ke cewa, idan haka ta kama, to NATO za ta tura  makamanta na nukiliyar zuwa kusa da iyaka da kasar Rasha.

“An ji Madam Liz Truss, Sakatariyar Harkokin Wajen Birtaniya na furta wannan zance a birnin Landan, inda ta kara da cewa NATO na cikin shirin gwabza yaki da Rasha,” inji Lavrov.

A cewar, “wannan mahawara ce da ke gudana a tsakaninku, ba wai mu ne muka bijiro da batun makaman nukiliya ko kuma barkewar yakin duniya na uku ba, suna furta wadannan kalamai ne a yunkurinsu na shafa wa Rasha kashin kaji, kuma dukkanin matakan da suke dauka kan kasarmu, suna yin hakan ne ba a kan ka’ida ba.”

Komai na tafiya daidai a Ukraine —Putin

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce yakin da ya kaddamar a Ukraine na tafiya yadda aka tsara.

Yana magana ne yayin wani jawabi da ya gabatar a ranar Alhamis.

Ya nanata cewa suna yaki ne da dakarun kasar ba wai fararen hulla ba, wadanda tuni gwamnatinsa ta ba wa damar ficewa daga wuraren da ake yaki.

Ya kara da cewa babban abun da suka sanya a gaba shine na ganin sun gurgunta tsaron Ukraine, da kuma kawar da barazanar da take kasar ke yi wa Rasha.