Daily Trust Aminiya - Za mu hukunta duk gidan man da ya rufe a Katsina -Kuniyar di
Subscribe

Za mu hukunta duk gidan man da ya rufe a Katsina -Kuniyar dillalai

Shugaban Kungiyar Dillalan man fetur na Jihar Katsina ya ce, kungiyar za ta hukunta duk wani gidan man fetur da aka rufe a fadin Jihar ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, musamman akan abin da ya shafi karewar man ko wani gyara.

Shugaban kungiyar Alhaji Abbas Hamza Maigoro, ne ya shaidawa wakilin Aminiya hakan a lokacin da aka tuntube shi don ganin irin yadda wadan su gidajen man suka fara rufe gidajen man na su musamman a cikin babban birnin Jihar.

Rufewar da ake gani na da nasaba da sanarwar da gwamnatin Jihar ta bayar na rufe dukkan iyakokin shigowa jihar a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Coronavirus da ta zamo wata annoba a duniya.

Sai dai a sanarwar da gwamnatin ta bayar na hana shiga ko fita a duk fadin jihar, bai shafi su motocin jigilar man da sauran na kayan masarufi da bukatuwar yau da kullum.

“Muna da mai a jihar Katsina mai yawa, saboda haka babu wani gidan man da zai rufe ya ki sayarwa jama’a sai fa in man ne ya kare ko kuma wata lalura daban. Amma in ba haka ba, duk wani gidan man da ya rufe da gangan, to za mu hadu da jami’an ‘Task Force’, mu bincika muddin muka samu rahoton faruwar hakan, domin hukunta kowane gidan mai”.

Alhaji Abbas, wanda ya jinjinawa gwamnatin Masari akan bayar da wannan dama, har ila yau, ya ce, “Duk da har yanzu bamu da tabbaci, amma akwai yuwuwar gwamnatin tarayya ta kara rage kudin man ya dawo kasa da Naira 100. To idan mai gidan mai ya rufe karshe yayi asara, domin da zarar an bayar da sanarwar ragewar, to dole a rage.”

Akan haka, Shugaban kungiyar ya ja hankalin masu gidajen mai da su ji tsoron Allah su kuma duba irin halin da jama’a suke ciki, duk abin da zasu yi kada su kuntatawa jama’a, domin a halin da ake ciki, man nan ya zama tamkar ruwa a jikin dan-adam.

More Stories