✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za mu hukunta masu tsokanar mata masu Abaya’

Hisbah za ta sa kafar wando da masu tsokanar mata masu sanya abaya.

Hukumar Hisbah ta sha alwashin daukar matakin ba sani ba sabo a kan duk mutumin da aka kama yana tozarta matan da ke sanya tufafi nau’in Abaya a Jihar Kano .

Hukumar ta bakin Babban Kwamandanta, Ustaz Haruna Sani Ibn Sina ta ce daukar matakin ya zama dole duba da yawan korafin da mata suka kawo mata a sakamakon sanya Abaya a ’yan kwanakin nan.

Babban Kwamandan ya bayyana cewar ya zama wajibi mutane su gane cewar Abaya kalma ce ta Musulunci, bai kyautu mutane na yin dan kira ko tozarta matar da ta yi kwalliya ko ta sanya tufafin ba.

Ustaz Harun Ibn Sina ya bayyana cewa Abaya tana daga cikin nau’in sutura da Musulunci ya yarda mata su yi amfani da ita.