✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu iya hukunta Tinubu kan ‘gorin’ da ya yi wa Buhari —Adamu

Sanata Adamu ya ce kamata ya yi Tinubu ya je ya ba Buhari hakuri.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyar na iya hukunta Asiwaju Bola Tinubu, jigo a jam’iyyar dangane da kalamai ‘marasa dadi’ da ya yi a kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A ranar Alhamis da ta gabata ce Tinubu ya ce shi ne ya zama ja gaba a yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi nasara a 2015, yana mai cewa, “Ba don ni ba da Buharin bai ci zaben ba.”

Tinubu ya bayyana hakan ne a masaukin shugaban kasa a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget din APC gabanin zaben fitar da gwani na jam’iyyar da za a gudanar a makon gobe.

Ya ce “bayan faduwa zabe har sau uku, Buhari ya yi koka yana mai cewa ba zai kara tsayawa takara ba, amma ni [Tinubu] na garzaya har Katsina na roki Buhari da ya sake tsayawa takara kuma zai yi nasara saboda ni da wasu za mu shige masa gaba.”

Wadannan kalamai dai sun janyo cece-kuce a fadin kasar, inda da dama ke zargin Tinubu da goranta wa Buhari da har wasu ke ganin  ya kamanta kansa da Allah mai jibinta lamurra.

Sai dai da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja ranar Asabar, Adamu ya ce, “Muna iya hukunta shi [Tinubu] kan kalaman da ya yi wa Shugaban Kasa.

An ruwaito shugaban jam’iyyar yana cewa ba su ji dadin kalaman ba musamman daga Tinubu da ake kira jagoran jam’iyyar.

“Bai kamata ya kawo zancen abin da bai shafi Buhari ba, har ya ambaci sunansa, wanda mutum ne da muke ganin kimarsa a rayuwar jam’iyyarmu,” in ji shi.

Ya ce kuskure ne ya ambaci Buhari a wurin da ba ya nan.

Daga baya Tinubu ya fito ya ce ba a fahimci kalamansa ba ne, yana mai cewa yana matukar mutunta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma ba zai taba raina shi ba.

Amma Shugaban APCn ya bayyana kalaman na Tinubu a matsayin “kururuwa bayan yaki” yana mai cewa kamata ya yi ya je ya ba Buhari hakuri.

“Ni ina ganin Tinubu ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ya yi kalaman,” in ji Abdullahi Adamu.

Shugaban na APC kuma ya ce dukkanin masu neman kujerar Shugaban Kasa mutum 23 za su yi takara a zaben fitar da gwani da jam’iyyar za ta gudanar a makon gobe, sabanin rahotannin da ke cewa an cire sunayen mutum saboda rashin cancanta.