✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kara wa ilimi kaso 50 a kasafin kudi na gaba —Buhari

Shugaban ya yi alkawarin ne a yayin taron Landan kan ilimi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kara wa bangaren ilimi rabin kason da aka yi wa bangaren a kasafin kudin shekara biyu masu zuwa.

Shugaban, a cewar kakakinsa, Femi Adesina, ya yi alkawarin ne a makalar da ya gabatar yayin taron kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Landan na kasar Birtaniya.

A cikin makalar mai taken ‘Kira ga shugabannin kasashen duniya kan kara wa ilimi kudin gudanarwa’, Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya kara kashi 50 cikin 100 a shekarun biyu masu zuwa.

Ya ce nan da shekarar 2025, ana sa ran samun karin kashi 100 a kan kasafin kudin ilimin Najeriya wanda wanda shi ne ma’aunin da kasashen duniya suka amince da shi.

Buhari ya jaddada goyon baya da jinjina ga shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya a kan kokarinsa na inganta ilimi a kasarsa.

Ya kara da cewa, “Dukanmu mun goyi bayan wannan yunkuri kuma muna kira ga masu ruwa da tsaki da ’yan kasuwa su kawo sabbin hanyoyi dan kara bunkasa ilimin fasaha da wayar da kan jama’a a kan hakan.”

Aminiya ta rawaito cewa taron wanda Firai Ministan Burtaniya, Boris Johnson da Uhuru Kenyatta suke jagoranta zai ba wa shugabannin kasashe damar tattaunawa don tallafa wa inganta tsarin ilimi a kasashe akalla 90 na duniya.