✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kare martabar dimokuradiyya a Zaben 2023 —DHQ

Dimokuradiyya ta zo kenan, kuma zama daram.

Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta yi alkawarin kare martabar dimokuradiyya da tabbatar da tsaro domin gudanar da Zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.

Aminiya ta ambato Shugaban DHQ, Janaral Lucky Irabor ne ya sanar a bikin Ranar Tunawa da ’Yan Mazan Jiya da aka gudanar a ranar Lahadin karshen mako a Abuja, babban birnin kasar.

Ya kara da cewa dimokuradiyya ta na nan daram a kasar domin haka sai inda karfinsu ya kare wajen tabbatar da hakan.

“Dimokuradiyya ta zo kenan, tsari ne da ke kafa gwamnatin da ’yan Najeriya suka zaba, kuma suka amince da ita.

“Ina tabbatar muku cewa, za a yi zabe cikin kwanciyar hankali, na kuma san kun san cewa ’yan sanda na sahun gaba a wannan fannin.”

Batun matsalar tsaro da wasu sassan Najeriya ke fama da shi na daga cikin babbar fargabar da ake nunawa a lokacin zaben da ke tafe.

Ko da yake, gwamnati da hukumomin tsaro na bayar da tabbacin yin duk abin da ya dace domin yin zaben cikin lumana.