✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Za mu kashe fasinjojin jirgin kasa idan gwamnati ta ki biya mana bukatu”

Aminiya ta gano cewa sun dauki bidiyon ne a gaban sansanin sojoji da ke Polwire a yankin Birnin Gwari

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjoji bayan harin da suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, sun yi barazanar kashe su muddin Gwamnatin Tarayya ta gaza biya musu bukatunsu.

A cikin wani faifan bidiyo da suka fitar ranar Laraba, mutanen da ke dauke da muggan makamai sun ce ba kudi suke bukata ba, gwamnatin ta san ko me suke nema.

Bidiyon wanda bai cika minti biyu ba dai ya nuna hudu daga cikin ’yan bindigar tare da daya daga cikin mutanen da suka sace – Shugaban Bankin Bunkasa Noma, Alwan Hassan.

Daya daga cikin ’yan bindigar, wadanda suke sanye da kakin sojoji, wanda ya yi magana da harshen Hausa, ya ce sun saki Shugaban bankin ne saboda shekarunsa, da kuma tausaya masa da suka yi, albarkacin watan Ramadan.

Aminiya ta gano cewa sun dauki bidiyon ne a gaban sansanin sojoji da ke Polwire a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, wanda aka kai wa hari ranar Litinin.

Sun dai yi amfani da daya daga cikin tankokin yakin da suka kona a bayansu wajen daukar bidiyon.

“Mu ne wadanda suka sace fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, ’yan kwanakin da suka wuce. Daga cikin mutanen da muka kama har da wannan mutumin da ya yi ta rokon mu, saboda haka mun sake shi saboda shekarunsa da kuma albarkacin watan Ramadan don ya koma wajen iyalansa.

“Amma ya kamata gwamnati ta fahimci wannan tausayi ne ya sa muka yi haka.”

Daga nan ne sai suka ba Alwan din damar ya ce wani abu, inda a wani dan takaitaccen jawabi ya ce tausayi ne ya sa suka sake shi.

“Ina mai tabbatar muku cewa na baro tarin mutane a wajensu, kuma suna bukatar taimakon gaggawa don a ceto su cikin gaggawa. Ina fatan gwamnati za ta tuntubi shugabanninsu don a samu a ceto su a kan lokaci,” inji Alwan.

Shi ma daya daga cikin ’yan bindigar ya ce, “Abin da ya fada gaskiya ne. Kada ku yi yunkurin bincikar mu, ko ku ce zaku ceto su, saboda kashe su karamin abu ne a wajenmu. Ba kudinku muke so ba, idan kudi muke so da ba mu kai harin ba ma kwata-kwata. Kun san abin da muke nema,” inji shi.