✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai mun ga bayan makiyan Najeriya —Gbajabiamila

Shugaban Majalisar ya ce za su su duk mai yiwuwa don kawo karshen makiyan Najeriya.

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce za su yi amfani da dukkannin abin da Najeriya ke da shi wajen yakar makiyan kasar.

Ya bayyana hakan lokacin da ya ke yi wa ’yan majalisa jawabi bayan dawowa daga hutun da majalisar ta yi a ranar Laraba.

“Matsalar tsaro ta kasance kalubalen da ta hana jama’ar Najeriya samun cigaban da ya kamata a ce sun samu a yanzu.

“Muna sanar da wanda suka mayar da kansu makiyan Najeriya cewar wannan majalisar za ta yi amfani da dukkannin abun da Najeriya take da shi wajen yakarsu, har sai mun ga bayansu,” a cewarsa.

Gbajabiamila, ya ce majalisar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace wajen ba wa jami’an tsaro dukkannin taimakon da suke bukata don yakar ta’addanci a Najeriya.

“A zaman da muka yi a baya mun tattauna manyan batutuwa da suka shafi matsalar tsaro kuma mun mika su zuwa gaba don daukar matakin da ya dace.

“Jagorancin majalisa ya aike wa Shugaban Kasa rahoton matakan da ya kamata a dauka kan sha’anin tsaro kuma ya ba mu tabbacin za a aiwatar.

“Za mu ci gaba da bibiya don tabbatar da daukar matakin da ya dace,” inji Gbajabiamila