✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kawo sojojin haya daga ketare idan Buhari ya gaza magance ta’addanci —El-Rufai

Na sha yi wa Buhari korafi kuma na rantse da Allah idan ba a dauki mataki ba za mu dauka da kanmu.

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya yi barazanar kawo sojojin haya daga ketare domin yakar ’yan bindiga da ke nokewa a cikin dazukan da ke kewayen Kaduna suna tafka ta’asa a duk lokacin da suka ga dama.

El-Rufai ya ce wannan ita kadai ce mafita muddin Gwamnatin Tarayya wadda Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta gaza kawo karshen matsalar taaddanci da ake fama da ita a kasar baki daya.

Gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya ke yi wa manema labarai bayani kan sakamakon ganawarsu da Shugaba Buhari, dangane da harin jirgin kasan da ya auku ranar Litinin wanda ya janyo asarar rayuka da dukiya.

El-Rufai ya ce harin ya yi sanadin mutuwar akalla fasinjoji tara da raunatar wasu 40 da kuma garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.

Ya kuma shaida cewa an samu tattaunawa tsakanin iyalai da wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai har yanzu ’yan bindigar ba su nemi kudin fansa ba, illa daga wajen mutum guda.

‘Ba ma biyan fansa’

El-Rufai ya ce su gwamnatin Kaduna ba sa biyan diyya ko kudin fansa don haka babu wannan batu a yanzu, ko a tattaunawarsu da shugaban kasa.

Gwamnan ya jadada cewa tun da fari sun aike da sakon gargadi zuwa ga hukumomin jirgin kasa cewa ‘yan Boko Haram sun shigo kuma suna tsara wannan hari.

Ya ce wannan ne dalilin da ya sa ya ce a takaita zirga-zirgar jirgin musamman in dai dare ya yi.

“Mun sha rubuta wasika ga hukumar zirga-zirgar jirgin kasa da sanar da su cewa Boko Haram za su kai hari kan jirgin.

“Sannan jirgin sojin sama sun je katari sun yi sansani inda helikwafta zai iya sauka da shan mai saboda idan wani abu ya faru su gaggauta kai sauki.

“Sai dai da yake daddare ne hakan ya kasance da wahala. Kuma dama maharan sun shirya sosai sun san jirgin da suke son kai wa hari, suna da labarin manyan mutane da ke cikin jirgi.”

La’akari da yadda ’yan bindiga ke ci gaba da tsananta kai hare-hare musamman a jihohin Yammacin Arewa, tsohon Ministan Abujan ya bayyana cewa gwamnonin Najeriya ba su da wani zabi a yanzu illa iyaka su dauki mataki da kansu.

“Na sha yi wa Shugaba Buhari korafi kuma na rantse da Allah idan ba a dauki mataki ba, to mu a matsayinmu na gwamnoni za mu dauki matakin kare rayukan al’ummar da kanmu.

“Idan har ya kai munzalin da za mu dauko sojojin haya daga ketare, to hakan za mu yi mu magance wannan kalubale.

Sai dai duk da wannan babatu, gwamnan ya ce a halin yanzu shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa cikin ’yan watanni masu zuwa komai zai zo karshe.

Kazalika, Gwamnan ya ce ya sake jaddadawa shugaba kasar matsayarsa na a kona dazuzzuka da wadannan ’yan ta’adda ke buya baki daya.

Ya shaida cewa wannan babban al’amari ne wanda ya kamata dazuzzuka da ’yan tadda suke a sakar musu bam a kashe kowa, a cewarsa.

“Na fada wa shugaba Buhari idan ba hakan aka yi ba to wallahi wannan hare-hare ba za su tafi ba, kuma suna iya tada Najeriya baki daya, saboda mutanen ba sa tsoron kowa daga jami’an tsaro har hukuma.

Suna samun kudi, suna bugun kirgi, me zai hana a karkashe su kawai, kowa ya san inda suke.

“Jami’an SSS na ba da rahotanni kullum a inda suke, ga abin da suke shiryawa. Abin da na zo sanar wa shugaban kasa kenan.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a shekarar 2015 ce aka zargi Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Goodluck Jonathan da kawo sojojin haya daga Afirka ta Kudu domin su yaki ’yan Boko Haram, sai dai tun a wancan lokaci gwamnatin ta musanta zargin.