✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kwashe duk maniyyatan Najeriya da suka rage —NAHCON

Da karfe 12:00 na daren Lahadin nan wa’adin rufe jigilar maniyyata zai cika.

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta sanar cewa za ta kwashe dukkan maniyyatan kasar da suka rage a kasa zuwa kasa mai tsarki.

NAHCON ta jaddada kwarin gwiwar ne yayin da ake shirin rufe jigilar maniyyatan zuwa Saudiyya a daren Lahadin nan.

Zuwa yanzu maniyyata fiye da 18,000 ne suke jiran a kai su Saudiyyar, yayin da hukumar ta NAHCON ta kwashe 25,361 kawai daga cikin fiye da 43,000 na maniyytan Najeriya.

Da karfe 12:00 na daren Lahadin nan wa’adin rufe jigilar maniyyata zai cika, kodayake wasu kamfanonin sufurin jirage sun samu karin awanni na ci gaba da aikin.

BBC ya ruwaito cewa, yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, NAHCON ta ce tana da kwarin gwiwar kwashe maniyyatan da suka rage zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.

Aminiya ta ruwaito cewa, maniyyatan aikin Hajji daga Najeriya kimanin 2,500 na fuskantar barazanar kasa sauke farali a aikin Hajjin bana.

Kungiyar Masu Jigilar Aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON) ta bayyana cewa, sama da maniyyata 2,500 da za su bi jiragen yawo 51 za su iya rasa aikin Hajjin 2022, saboda jinkirin  biyan su kudin guzuri.

Rahotanni na nuna kamfanonin sun tura kudin ta asusun ajiya na bai-daya na Hukumar Aikin Hajjin ta Kasa (NAHCON) da ke Babban Bankin Najeriya (CBN) domin tura wa kamfanonin kula da alhazai a da ke Saudiya.

Ana ba wa maniyyata kudin guzuri ne domin biyan kudin masauki da abinci da kuma na zirga-zirga, da kuma biyan kudin biza.

Aminiya dai ta gano cewa, matukar ba a turawa masu jiragen yawon kudaden ba, babu yadda za su iya kammala tsare-tsarensu da kamfanonin kula da alhazai a Saudiyyan.

Kimanin maniyata 42 ne da suka bi jiragen yawo daga Kano dai suka isa Kasa Mai Tsarkin a ranar Talata ba tare da tabbatar musu da Bizar su ba.

To sai dai da saukarsu a kasar, aka jibge su a filin jirgin Muhammad Bn AbdulAziz da ke Madina aka dakatar da su har tsawon kwan guda, kafin daga bisani hukumar NAHCON ta shiga tsakani.

Manajan kamfanin jirgin yawon, Malam Kabiru Sani Babanyaya ya ce kamfaninsa ya yi duk mai yiwuwa ne ya tura maniyatan da suka bi ta hannunsu ne, saboda da sun rasa jirgin Saudi Airline da ya tashi ranar Talata, to za su tafka asarar Naira milyan 50.