✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu kwato dubban kadarorin Hukumar Gidan Waya — Pantami

Mun karbo wani fili da Gwamnatin Kaduna ta kwace shekara da shekaru.

Ministan Sadarwa da Habaka Tattalin Arzikin ta Fasahar Zamani, Dokta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce ma’aikatarsa za ta tabbatar da kwato kadarori fiye da dubu uku na hukumar aike wa da sakonni ta gidan waya, NIPOST, da suke warwatse a fadin kasar nan.

Pantami ya nunar da cewa da dama daga cikinsu sun lalace wasu kuma an cinye su.

Ministan ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da bude wasu shaguna 164 da ofisoshi 16 da  bandakai da wajen cin abinci da hukumar NIPOST ta gina a Gombe domin kara samar wa kanta kudaden shiga.

Ya yi kira ga jama’ar jihar da su kama hayar shagunan domin gudanar da kasuwanci saboda wajen yana kan hanya kuma idon jama’a ne.

Ya ce a matsayinsa na Minista mai kula da hukumar zai yi dukkan mai yiwuwa wajen kwato duk wata kadara mallakinta da aka cinye sannan a gina wajen domin kara samar wa da gwamnati kudaden shiga.

A cewar Pantami, akwai wani filin hukumar NIPOST a Kaduna da gwamnati ta karbe shekara da shekaru amma ya yi amfani da damarsa ta Minista ya zauna da Gwamna Nasiru El-Rufa’i inda ya karbo wa NIPOST filin, da sharadin a gina cikin lokaci ko gwamnatin jihar ta sake kwace shi.

Dokta Isa Ali Pantamin ya jinjina wa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya ce take ciyar da kasar gaba da ayyukan raya kasa.