✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu magance matsalar Guinea da kanmu — Doumbouya

Doumbouya ya ce suna bai wa Conde cikakkiyar kulawa.

Shugaban Mulkin Sojin Guinea, Mamady Doumbouya ya ce, kasarsa za ta iya magance matsalarta da kanta.

Kalamansa suna zuwa ne kwanaki kalilan da Kungiyar ECOWAS ta tsananta matsayarta a kan gwamnatin kasar.

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta dakatar da Guinea a matsayin mambar kungiyar tare da lafta wa manyan sojojinta takunkumi saboda juyin mulkin da suka yi a ranar 5 ga Satumba wanda ya kawo karshen shugabancin Alpha Conde.

ECOWAS ta bukaci sojojin su gaggauta sakin Conde mai shekara 83 da suka yi masa daurin talala bayan tumbuke shi daga kujerar mulki.

Tuni kungiyar ta nada jakada zuwa Guinea tare da bukatar gudanar da zabe cikin wata shida domin mayar da mulki ga farar hula.

A hirarsa da aka watsa ta talabijin, Doumbouya ya ce, suna bai wa Conde cikakkiyar kulawa, amma al’ummar Guinea ne kadai za su iya fayyace makomarsa.

Doumbouya wanda aka rantsar a matsayin Shugaban Rikon Kwarya a watan jiya, ya ce, yana adawa da matakin da ECOWAS ta dauka na nada jakada na musamman da kuma wa’adin gudanar da zabe cikin wata shida.

Doumbouya ya kara da cewa, suna da cikakkiyar basirar magance matsalarsu domin kuwa kasarsu ba ta cikin rikici, hasali ma kasa ce wadda makomarta ke hannunta