✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu maido da shingen bincike —’Yan sanda

Mun gargadi jami'anmu su guji cin zarafin mutane.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwar da ke bayyana bukatar dawo da shingen binciken ababen hawa domin tsaurara matakan tsaro.

Babban Sufeton ’yan sanda, IGP Alkali Usman Baba ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar rahoto kan al’amuran tsaro daga manyan jami’an na shiyoyi daban-daban a ranar Lahadi.

A cewarsa, akwai bukatar a tsaurara matakan tsaro a muhimman wurare kamar makarantu da asibitoci a daukacin kasar, a yayin da ake ci gaba da samun karuwar ayyukan ta’addanci.

Alkali Baba ya ce hakan zai bayar da damar duba ababen hawa a lokacin da za su shiga gine-ginen gwamnati.

Kazalika, Alkali Baba ya nemi hadin kan ’yan kasa wajen bai wa jami’ansa goyon bayan gudanar da ayyukansu na tsare rayuka da dukiyoyi, a yayin da za su rika gudanar da sintiri ba dare ba rana.

Sai dai shugaban ‘yan sandan ya umurce jami’an da alhakin hakan zai rataya a wuyansu da yin aiki cikin kwarewa ba tare da cin zarafin ‘yan kasa da ma amsar na goro ba.

Wannan sabon matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar da ke da mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, ke shirye-shiryen tunkarar zaben gama gari a shekarar da ke tafe.

Al’umma a Najeriya da ma masu rajin kare su na martani a game da wannan mataki na maido da shingen bincike, wanda suka ce duk da alkawarin da mahukuntan kasar suka yi na maido da da’a a tsakanin jami’an ‘yan sanda har yanzu suna ci gaba da tsohuwar dabi’arsu wacce a shekarar 2020 ta jefa kasar cikin hargitsi da ya yi sanadiyar rayukan mutane musamman ma a Jihar Legas.