Za mu mallaki na’urorin kakkabo makamai masu linzami —Jamus | Aminiya

Za mu mallaki na’urorin kakkabo makamai masu linzami —Jamus

Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz
Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz
    Ishaq Isma’il Musa

Jamus na shirin mallakar na’urorin kakkabo makamai masu linzami daga Isra’ila, a yunkurinta na mallakar makaman kare sararin samaniyarta daga duk wata barazana ta abokan gaba.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ne ya bayyana haka a yayin wani jawabinsa ta gidan talabijin, inda ya ce yanzu hakan suna tattaunawa kan wannan mataki.

Tun bayan barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, Jamus ta ambaci ware makudan kudade na sake fasalta fanninta na tsaro da nufin kare kanta.

Sabon makamin mai suna Arrow 3 mallakar kasar Isra’ila ka iya kare kasar Jamus har ma da sauran wasu kasashe makwabtanta irinsu Poland da Rumaniya da wasu kasashen yankin Batik, in ji Andreas Schwarz wani na kusa a Majalisar Dokoki ta Bundestag.